Sakamakon binciken da ‘Global Burden of Disease’ ta gudanar ya nuna cewa Afrika na daga cikin barayin duniya dake samun karuwa a yaduwar cutar dajin dake kama nono inda kasar Equatorial Guinea ta samu karin kashi 312% karin da ya fara daga shekarar 1990 har zuwa yanzu.

An wallafa wannan sakamakon a ‘Lancet’ ranar Litini sannan an gudanar da binciken ta hanyar tantance takardun dake dauke da yawan mutanen dake fama da cutar da tattaunawa da masu fama da cutar, iyalen sun da jami’an lafiyan dake Kula da masu fama da cutar.

Kashi ‎ 30% Ne Kwai Na Yaran Daya Kamata Suje Makaranta Suke Zuwa A Arewacin Najeriya  ‎ ‎ ‎— Farfesa Shehu

Sakamakon binciken ya gabatar da bayanai kan yawan mutanen dake fama da cutar a Duniya, barayin duniya da kasashe sannan da matsalolin da ka iya haifar da cutar daga shekarun 1990 zuwa 2023 a kasashe 204 tare da gabatar da hasashe game da cutar nan da shekarar 2050.

Sakamakon binciken ya nuna cewa Afrika na yawan samun karuwa a yaduwar cutar daga shekarun 1990 zuwa 2023 inda kasar Equatorial Guinea ta samu karin kashi 312% na yaduwar cutar da karin kashi 212% a yawan mutanen da cutar ke kashewa.

Sauran kasashen Afrika da suka samu karuwan yaduwar cutar sun hada Ethiopia- 207%, Masar -189%, Jamhuriyar kasar Kongo -160% da Mauritania -141%.

Kasar Uganda -135%, Mali -133% da Liberia -129%.

Yaduwar Cutar A Najeriya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa Najeriya ta ci gaba da samun karuwa a yaduwar da yawan mutanen da ke mutuwa a dalilin cutar.

A shekarar 2024 mutum 53,500 ne suka kara kamuwa da dajin dake kama nono wanda hakan ke nuna karin kashi 542.9% daga 1990.

Binciken ya nuna cewa mutum 72.1 cikin mutum 100,000 ne suka kamu da cutar wanda hakan ke nuna karin kashi 108.8% daga 1990.

Cutar ya yi ajalin mutum 26,200 a shekarar 2023 wanda hakan ke nuna karin kashi 408.3% daga 1990.

 

Mutum kashi 38.7% daga cikin mutum 100,000 ne suka mutu a dalilin cutar karin kashi 73.5% daga 1990.

 

Wadannan alkaluma sun tabbatar da wanda PREMIUM TIMES ta gabatar na yiwuwar samun karin kashi 38% a yaduwar cutar a nan da 2025 a Duniya sannan kasashen dake tasowa har da Najeriya za su fi samun babban kaso na yawan yaduwar cutar.

Sakamakon binciken ya tabbatar da matsaloli da suka hada da gazawan kudirorin dakile yaduwar cutar da rashin fada bincike domin inganta fannin lafiya na daga cikin matsalolin da ya sa cutar ke kisan mata a Najeriya musamman idan aka hada da matsalolin rashin yin gwajin cutar wanda zai taimaka wajen gano cutar da wuri, rashin ingantacen fannin lafiya da tsadan farashin kiwon lafiya.

Hasashen Yaduwar Cutar daga Nan Zuwa 2025 a Duniya.

Dajin dake kama nono na daga cikin cututtukan dake kisan mata a Duniya.

Ana zaton cewa mata miliyan 2.3 ne suka kamu da cutar a 2023 inda kashi 73% daga cikin su na daga kasashen dake tasowa.

Sakamakon binciken ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar ke kashewa a Duniya ka iya karuwa zuwa kashi 44% daga 764,00 a 2023 zuwa kusan mutum miliyan 1.4 a 2050 inda mafi yawan su na kasashen dake tasowa.

Za kuma a samu karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da cutar a Duniya daga miliyan 2.3 a 2023 zuwa mutum miliyan 3.5 a 2050.

A shekarar 1990 zuwa yanzu an samu karuwar yaduwar cutar a tsakanin matasan mata masu shekaru 20 zuwa 54 sannan tsofaffin mata sun ci gaba da kamuwa da cutar.

Masu gudanar da bincike sun shaida cewa nan gaba za a samu canji a rukunin matan dake kamuwa da cutar.

Abubuwan dake Hadassa Cutar a jikin Mata.

Binciken ya nuna kashi 28% na mutanen dake kamuwa da cutar na kamuwa da cutar a dalilin matsaloli shida da suka hada da zukan taba sigari, hawan jini da yawan kiba.

Sauran matsaloli sun hada da yawan cin nama musamman naman shannu, Shan barasa, da rashin motsa jiki.

Binciken ya tabbatar cewa guje wa Shan barasa, zukan taba sigari, rage yawan cin naman shanu da motsa jiki na daga cikin matakan da za su taimaka wajen kare mutum daga kamuwa da cutar.

Jagoran wadanda suka gudanar da binciken Lisa Force ta yi kira kan hada hannu domin daukan matakan da suka fi dacewa domin dakile yaduwar cutar.

 

Lisa ta jadadda mahimmancin inganta fannin lafiya musamman fannin kula da masu fama da cutar tare da inganta yin gwajin cutar domin hakan zai taimaka wajen ganin cutar a jikin mutane a kasashen Duniya.

 

Ta kuma yi kira da a inganta kudirin samar da lafiya ta gari wa kowa da kowa da rage farashin kula da masu fama da cutsr domin tallafawa mutane musamman masu fama da cutar.

 

Premium times 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version