Daga Salisu Ibrahim Fagge tare da haɗin gwiwar Abbas Ibrahim, Mohammed Kabir Yau, Abdullahi Yusuf, Mustapha Muhammad da Kabiru Fulatan

 

‎Kasuwancin dabbobi a Kano na kara bunƙasa cikin sauri, yayin da buƙatar nama, madara da fata ke ƙaruwa a sassan Najeriya.

‎Amma duk da wannan ci gaba, wani bincike na musamman ya nuna cewa ana fuskantar babbar barazana ta ɓoye sakamakon yawaitar amfani da wani sinadarin magani da ake yiwa lak’abi da (kira) “Sha Ka Fashe.”

Jam’iyyun Adawa Sun Yi Fatali Da Sabuwar Dokar Zabe Ta 2026 Wacce Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ita

‎Binciken ya gano cewa wasu ’yan kasuwar dabbobi na amfani da wannan sinadari domin sa shanu da tumaki su K’ara kiba cikin gaggawa, don su jawo hankalin masu saye a kasuwa.

‎Rahotanni sun nuna cewa “Sha Ka Fashe” da aka fi dangantawa da ƙara kiba a jikin ɗan adam, yanzu ana ba dabbobi domin su yi girma cikin kankanin lokaci.

‎Masana sun yi gargadin cewa hakan na iya cutar da lafiyar jama’a, domin samuwar magunguna a nama na iya haifar da matsaloli masu tsanani, ciki har da cututtuka.

‎Wasu masu sayen dabbobi sun koka da asarar dukiya bayan sayensu. Dabbobin a bayyane masu ƙoshin lafiya ne, amma daga baya sai su kamu da rashin lafiya ko ma ta kai ga mutuwarsu cikin k’ank’anin lokaci.

‎Malam Muhammad Balarabe ya ce ya sayi saniya cikakkiya mai ƙiba a zahiri ga alamun ƙarfi da lafiya a ido, amma cikin kwanaki kaɗan ta kamu da gudawa mai tsanani kuma ta mutu. Ya ce irin wannan lamari na buƙatar Gwamnati ta dauki matakan gaggawa domin maganta lamarin.

‎Jami’an Hukumar Kula da abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC sun ce sun kama magungunan jabu, kuma sun rufe masana’antun da ke samar da ire iren wadannan magungunan dabbobi ba tare da rajista ba, tare da gurfanar da masu laifi a kotu.

Ana ta bangaren ma’aikatar kula da kiwon dabbobi ta jihar Kano, ta bullo da tsari domin yin rajistar wuraren kiwo da bibiyar masu sayar da magungunan dabbobi domin a inganta lafiyar al’umma.

‎Masana da masu ruwa da tsaki sun ce idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, matsalar za ta iya zama barazana ga lafiyar jama’a, tattalin arziki da Kuma samar da  abinci.

‎Sun buƙaci a sami tsauraran dokoki kan amfani da magungunan dabbobi, kuma a baiwa ‎wayar da kan jama’a a kan haɗarin nama maras inganci muhimmanci, sannan a tallafa wa manoma masu bin ƙa’ida, da kafa cikakkiyar mayanka da za ta gudanar da ayyukanta bisa tsarin halal, a inda ƙwararru ma’aikata za su rinka kula da mayankar.

‎Yayin da kasuwancin dabbobi ke ci gaba da bunƙasa a Kano, jama’a na fatan a ɗauki mataki cikin gaggawa domin hana wannan matsala ta zama barazana ga rayuwar al’umma..

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version