Dakarun Sojin Najeriya da ke cikin runduna ta musamman mai yaƙi da ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso yammacin ƙasar wato Fansar Yamma sun sanar da nasarar kashe tarin ƴan ta’addan Lakurawa a jihar Kebbi a dai dai lokacin da ƴan ta’addan suka nufaci kai wani hari a jihar Kebbi.
Masanin tsaron yankin tafkin Chadi Zagazola Makama da ke sanar da wannan nasara ta dakarun Sojin Najeriyar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce tun da farko ƴan ta’addan suka ɗauki azamar kai hari wata kasuwar ƙauye ce a safiyar jiya Lahadi da ke garin Daɗin kowa a jihar Kebbi amma kuma Sojin Najeriyar suka yi musu tara-tara tare da kashe da dama daga cikinsu.
Ana ci gaba da matsa wa DSS lamba kan ta saki Walida
Makama ya bayyana cewa da farko ƴan ta’addan Lakurawan sun toshe hanyoyi da nufin zagaye yankin da suke son kaiwa harin, gabanin juyewar lamarin zuwa kansu.
Majiyoyi sun ce cikin gaggawa dakarun Sojin Najeriyar suka kai ɗauki bayan samun bayanai daga al’ummar yankin game da yunƙurin harin na Lakurawa, lamarin da ya juye zuwa ga musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu
A cewar bayanai daga majiyoyin yankin ruwan wutar da sojin Najeriyar suka yiwa ƴan ta’addan ba ƙaƙƙautawa ne ya tialsta musu janyewa cikin hanzari kodayake sojojin sun kashe da dama daga cikinsu yayinda wasu suka tsere da raunuka a jikinsu.
