Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanya dokar takaita zirga-zirga a ƙananan hukumomin birnin kano da Ungogo na tsawon awanni 18, gabanin zaɓen cike-gurbi na ‘yan majalisar dokokin jihar kano da za a gudanar a yau Asabar.

’Yan sandan sun ce dokar, wadda za ta fara aiki daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa ƙarfe 6:00 na yamma a ranar Asabar, ta shafi motocin haya da masu zaman kansu, babura masu ƙafa uku da kuma babura masu kafa biyu, a matsayin wani mataki na inganta tsaro domin tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Jihohin Najeriya da suka fi yin kasafin kuɗi mai tsoka a 2026

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya ce an ɗauki matakin ne bayan wani taron nazarin tsaro da Kwamitin inganta tsaro kan harkokin zabe ya gudanar.

Sai dai an tsame motocin da ke gudanar da ayyukan gaggawa daga cikin dokar, wanda suka hada motocin asibiti, da na kashe gobara, da kuma motocin jami’an zaɓe da masu sa ido da aka tantance, a lokacin da dokar ke aiki

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version