Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr Abdullahi Muhammad Getso, ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu tarbiyya da nagarta da su fito su shiga harkokin siyasa, domin gyara shugabanci a ƙasar.

‎Dr Getso ya yi wannan kira ne yayin hudubar Juma’a a Masallacin Jami’ur Rahman Jumaat da ke Kundila, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane nagari da masu cancanta ke gujewa shiga takara, lamarin da ke barin siyasa a hannun masu son zuciya da rashin kishin kasa.

Caca na Ci Gaba da Shafar Matasan Arewa, Hisbah Ta Yi Gargadi

‎“Hakkin al’umma ne su gano shugabanni nagari, su ƙarfafa musu gwiwa su nemi shugabanci, domin al’umma ta amfana da adalcinsu da gaskiyarsu,” in ji Dr Getso.

‎Malamin ya jaddada cewa canjin al’umma zai yiwu ne idan shugabanni masu kyakkyawan hali suka tsaya tsayin daka, tare da goyon baya da wayar da kan jama’a.

‎Ya kuma soki halayen wasu ‘yan siyasa da ke amfani da mulki wajen almundahana da dukiyar jama’a, inda talakawa ke ɗaukar nauyin rashin adalci da rashin shugabanci mai kyau.

‎Dr Getso ya bayyana muhimman siffofin shugabanci nagari, wanda ya haɗa da:

‎Adalci, Gaskiya, Kare dukiyar jama’a, Ƙin cin hanci da rashawa, BuɗeBuɗe ƙofa ga shawarwarin masana domin ci gaban al’umma.

‎Hudubar ta ƙare ne da addu’o’i na samun zaman lafiya, ci gaba, da wadata ga Najeriya baki ɗaya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version