Shugaban Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari na jihar Kano, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, ya yi Allah-wadai da kisan matar aure da ’ya’yanta shida a Jihar Kano.

‎An kashe Fatima Abubakar mai shekaru 35, tare da ’ya’yanta a gidansu da ke Dorayi Gidan Kwari a ranar Juma’a.

Rikicin Cikin Gida Ne Zai Iya Tura Abba Kabir Yusuf Barin NNPP — Shugaban Jam’iyyar a Kano

‎‎Sanata Doguwa ya yi wannan bayani ne yayin wani taron “Manema Labari” da aka gudanar a Kano ya bayyana lamarin a matsayin abun tashin hankali, kuma ya ce lamarin ya taɓa zuciyar al’ummar Kano.

‎“Na shiga matuƙar damuwa da girgiza bisa kisan gillar da aka yi wa wata uwa da ’ya’yanta shida a Kano.

‎­“Wannan mugun aiki bai tsaya kan waɗannan mutane ba, ya karya tasirinmu na zaman lafiya da girmama rayuwar ɗan Adam,” in ji shi.

‎Shugaban Jam’iyyar ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar da sauran waɗanda lamarin ya shafa, tare da yin addu’a ga mamatan.

‎“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan mamatan, da al’ummar Dorayi da Chiranchi, da kuma ɗaukacin al’ummar Jihar Kano.

‎“Allah Ya gafarta musu, Ya bai wa iyalansu haƙuri da juriyar jure wannan babban rashi,” in ji shi.

‎Ya kuma yi kira ga gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabanni da su haɗa kai wajen kare rayuka da hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version