Majalisar Dokokin Jihar Legas ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 4.4, bayan shafe lokaci tana gudanar da tattaunawa mai zurfi da nazari kan abubuwan da ke cikinsa.

Majalisar ta bayyana cewa ta amince da kasafin ne domin ganin yadda zai taimaka wajen bunƙasa rayuwar al’ummar jihar, musamman ta fuskar samar da ababen more rayuwa, inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya, da kuma haɓaka tattalin arziki.

Yan siyasan Arewa da malaman addinin Arewa da sarakunan Arewa su ne suka sayar da Arewa ‎ ‎—Naja’atu Muhammad

Shugaban Majalisar, Mudashiru Obasa, ya ce ‘yan majalisar sun tabbatar da cewa kasafin kudin na shekarar 2026 ya kasance mai mayar da hankali kan jin daɗin al’umma tare da tabbatar da ci gaba mai dorewa.

A cewarsa, majalisar ta yi cikakken nazari kan kasafin, inda ta gano cewa zai taimaka wajen samar da muhimman ayyuka kamar su gine-ginen tituna, bunƙasa harkar sufuri, ilimi, kiwon lafiya da gidaje, tare da buɗe sabbin hanyoyin samun kuɗaɗe ga mazauna jihar.

Obasa ya ƙara da cewa kasafin zai taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi da kuma bunƙasa kasuwanci, wanda hakan zai ƙara inganta tattalin arzikin jihar gaba ɗaya.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Legas cewa majalisar za ta ci gaba da sanya ido sosai kan aiwatar da kasafin, domin tabbatar da cewa an kashe kuɗaɗen cikin gaskiya, adalci da kuma amfanin jama’a.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version