Shehin malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya soki farmakin saman da Amurka ta kai kan sansanonin ’yan ta’adda a Arewa maso Yammacin Najeriya, yana cewa hakan na iya ƙara rarraba al’umma tare da tauye ikon ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa sojojin Amurka sun kai hare-hare masu tsanani, yayin da Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da haɗin gwiwar tsaro da musayar bayanan sirri da Amurka.
Jaridar Punch ta ruwaito wani rubutu da ya wallafa a Facebook, ya nemi gwamnati ta dakatar da haɗin gwiwar soji da Amurka, ta nemi taimakon ƙasashen China, Turkiyya da Pakistan.
Ya kuma ce jefa bama-bamai kaɗai ba zai magance ta’addanci ba, yana mai cewa Najeriya na da isassun sojoji don gudanar da ayyukan ƙasarta, tare da zargin cewa hare-haren a Sokoto na iya ƙara tayar da hankali da rarrabuwar kai a ƙasar.
