Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), a Gidan Gyaran Hali na Kuje, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan bukatar belin sa.
Alkalin kotun Mai Shari’a Emeka Nwite, ya kuma umarci a tsare ɗan, Abubakar Malami, da kuma daya daga cikin matan sa, Bashir Asabe, wadanda suke fuskantar shari’a tare da shi.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan sauraron muhawara daga bangaren lauyoyin kare wadanda ake tuhuma, karkashin jagorancin Joseph Daudu (SAN), da kuma bangaren masu gabatar da kara, wanda Ekele Iheneacho (SAN) ke jagoranta.
Alkalin ya bayyana cewa za a ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma a gidan yari na Kuje ne har sai kotu ta yanke hukunci kan bukatar belin su.
