Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda ba’a bayyana sunan sa ba, na fuskantar bincike kan zargin cewa yana da alaƙa da wasu jami’an soja da ake tsare da su bisa zargin shirin juyin mulki.
Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa ana zargin tsohon gwamnan da taimaka wa da kuɗi wajen shirya juyin mulkin da aka ce an tsara shi a gudanar ranar 25 ga Oktoba.
Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani
Rahotanni daga wasu kafafen labarai sun ce jami’an da ake tsare da su ciki har da Brigediya Janar, Kanal, da wasu duk suna ƙarƙashin ofishin mai ba wa shugaban shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (ONSA).
Wata majiya ta tabbatar cewa bincike yana gudana karkashin Hukumar Leken Asirin Soji (DIA), tare da wakilai daga dukkan rundunonin sojoji.
Sai dai Hedikwatar Tsaro ta ƙaryata rahotannin, inda ta ce ta kama jami’an ne saboda “saɓa ƙa’idojin aiki” ba wai saboda yunkurin juyin mulki ba.
DHQ ta ce rahoton juyin mulki karya ne, kuma ta tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya tana nan da cikakken biyayya ga kundin tsarin mulki da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Majiyoyi daga Nasarawa sun bayyana cewa ɗaya daga cikin jami’an da ake bincike ɗan wani tsohon gwamna ne, kuma iyalinsa sun bayyana damuwa kan lamarin.
A halin yanzu, an ce ana sa ido kan wasu ‘yan siyasa daga arewa da kudu bisa yiwuwar suna da hannu a lamarin.
