A makon da ya gabata, wasu jihohi biyu da babban birnin tarayya, Abuja, sun fuskanci barkewar cututtuka daban-daban, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma da hukumomin lafiya a Nijeriya.
Adamawa: Cutar Kuraje Ta Buruli Ulcer Ta Kashe Mutum Bakwai
Jihar Adamawa ta samu barkewar cuta mai zagwanye naman jiki, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cutar a matsayin Buruli Ulcer, wadda ake samun ta a karkara musamman wuraren da ke kusa da ruwa.
Dr. Adesigbin Olufemi na shirin kasa na dakile cutar tarin fuka da kuturta a Nijeriya ya bayyana cewa, an samu mutane 67 da ke dauke da cutar, yayin da za a yi wa mutum 8 tiyata. “Ba a gano dalilin barkewar cutar ba, amma bincike na ci gaba,” in ji shi.
Abuja: Zazzabi Mai Aman Jini Ya Jefa Jama’a Cikin Fargaba
Babban birnin tarayya, Abuja, ya fuskanci barkewar wata cuta da ke haddasa zazzabi da aman jini. An samu mutum biyu a asibiti tare da alamun cutar da suka hada da zubar jini daga baki, hanci da dubura.
Bayanan farko sun nuna cewa daya daga cikin mutanen ya yi tafiya zuwa Rwanda kafin ya fara fuskantar alamun cutar. Hukumomin NCDC sun fara gwaje-gwaje don gano ko cutar na da alaka da Ebola, Marburg, Dengue ko Lassa.
Hukumomi sun yi gargadi ga jama’a da su kula da shigi da ficin mutane, musamman a wuraren kasuwanci da taron jama’a.
Kaduna: Barkewar Mashako Ta Tilasta Rufe Makarantu
A jahar Kaduna, cutar Mashako ta kashe yara biyu a Karamar Hukumar Birnin Gwari, inda aka rufe makarantun jihar na tsawon mako guda.
Kwamishiniyar lafiya, Dr. Umma Kulthum Ahmed, ta ce rufe makarantu mataki ne na hana yaduwar cutar a tsakanin dalibai. Fiye da mutane 40 aka killace, wasu kuma daga cikinsu aka sallama daga asibiti.
Hukumomi sun yi kira ga al’umma da su kara tsaftar muhalli, bin ka’idojin lafiya, da kuma sanar da asibitoci duk wani mutum da ya fara fuskantar alamun cuta. Barkewar wadannan cututtuka uku ya nuna cewa akwai bukatar a dage wajen wayar da kan jama’a da kuma hanzarta dakile yaduwar cutuka.

