Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya aike da sunayen mutane 6 zauren majalissar dokoki ta Kano domin tantancewa don  Nada su  mukamin kwamishina kuma Yan majalissar zartarwar Sa.
Hakan na  kunshe ne  a cikin wata wasika da gwamnan ya aikewa kakakin majalissar Wanda kuma ya karanto yayin zaman majalissar na  Yau.
Daga  cikin wadanda za’a nada  mukamin kwamishinan akwai  Shehu Wada Sagagi, Ismail Danmaraya, Dahiru Hashim Muhammad, Gaddafi Sani Shehu, Abdulkadir Abdussalam da kuma Ibrahim Wayya.
Zauren majalissar ya bukaci wadanda za’a Nada dasu gaggauta aikewa zauren majalissar kwafin takardur su  kafin tashi daga  aiki a yau.
Sannan zauren majalissar ya bukaci dasu hallara a gobe  domin tantance Su.
Share.
Leave A Reply

Exit mobile version