Gwamnatin Jihar Kano ta ce a shirye take ta tallafa wa duk wani yunkuri da zai taimaka wajen kawar da matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da gidauniyar The Recovery Hub, wadda aka kafa domin taimaka wa masu fama da matsalar shaye-shaye da kuma wayar da kan al’umma kan illolin miyagun ƙwayoyi.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na ɗaukar matsalar shaye-shaye da matuƙar muhimmanci, saboda illar da take haifarwa ga lafiyar al’umma, musamman matasa.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shirye da ƙungiyoyin da ke da manufar yaƙi da shaye-shaye, tare da haɗa hannu da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile matsalar.
“Gwamnati a shirye take ta taimaka wa duk wani yunkuri da zai taimaka wajen kawar da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi,” in ji kwamishinan.
Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro, ƙwararrun ma’aikatan lafiya, ƙungiyoyin fararen hula da al’umma wajen samun nasara a yaƙi da matsalar.
A nasa jawabin, Shugaban gidauniyar The Recovery Hub, Dr Abdullahi Akilu, wanda likitan ƙwaƙwalwa ne a Asibitin Dawanau da ke Kano, ya nuna damuwa kan yadda matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke ƙara yaɗuwa a tsakanin al’umma.
Dr Akilu ya ce an kafa gidauniyar ne domin wayar da kan jama’a kan illolin shaye-shaye, da kuma samar da tallafi da kulawa ga mutanen da ke fama da matsalar.
Ya ce gidauniyar za ta kuma taimaka wa waɗanda suka samu sauƙi daga shaye-shaye wajen farfaɗowa da komawa cikin al’umma.
A cewarsa, matsalar miyagun ƙwayoyi ta zama babbar barazana ga al’umma, don haka ake buƙatar haɗin gwiwar gwamnati da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin magance ta.
Shi ma Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwar Hukumomin Jihar Kano kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Fataucin Haramtattun Abubuwa, Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce kwamitin zai yi aiki tare da The Recovery Hub domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar.
Muhuyi ya ce haɗin gwiwar hukumomi da ƙungiyoyin da ke taimaka wa masu fama da shaye-shaye na da matuƙar muhimmanci wajen rage matsalar da kuma kare matasa daga faɗawa cikin tarkon miyagun ƙwayoyi.
Ya yi kira ga iyaye da malamai da shugabannin al’umma da su ƙara ƙoƙari wajen wayar da kan matasa kan illolin shaye-shaye.
Taron ƙaddamar da gidauniyar ya samu halartar wakilan hukumomin tsaro da dama, da ƙungiyoyin lafiya, likitoci da sauran masu ruwa da tsaki. Daga cikin mahalarta akwai wakilan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, manyan likitoci daga Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, wakilan Asibitin Dawanau da kuma Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA).
Haka kuma, wakilan ƙungiyoyin fararen hula, ciki har da Youth Awareness Against Drug Abuse Initiative da Yan Jarida sun halarci taron, inda aka jaddada muhimmancin haɗin gwiwar hukumomi da ƙungiyoyi wajen yaƙi da matsalar shaye-shaye da wayar da kan al’umma, musamman matasa, samar da kulawa ga masu fama da matsalar da kuma taimaka musu wajen komawa cikin al’umma.

