Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar Labour Party (LP), Alhaji Hamisu Santuraki, ya yi alkawarin kafa Hukumar Kula da Hayar Gida da ’Yan Hayar Gida, idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027.
Santuraki ya ce manufar hukumar ita ce dakile ƙarin kuɗin haya ba bisa ƙa’ida ba da kuma kare ’yan haya daga cin zarafi da sauran matsalolin da suka shafi haya.
Ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakinsa, Comrade Abbas Ibrahim, inda ya ce hukumar ba za ta sanya farashin haya iri ɗaya ga dukkan gidaje ba, sai dai ta tsara farashi bisa la’akari da wurin da gida yake, irin gidan, girmansa, yanayinsa da kayan more rayuwa.
Ya ce za a yi rajistar masu gidaje da kadarorin haya, sannan a ba dillalan gidaje lasisi tare da tsara kuɗin dillanci da sauran ka’idojin gudanar da sana’ar.
Santuraki ya ƙara da cewa hukumar za ta samar da tsarin kai ƙorafi da sasanta rikicin haya, musamman kan ƙarin haya ba bisa ƙa’ida ba, korar ’yan haya, tsadar kuɗin dillanci da cin zarafi.
A cewarsa, za kuma a samar da wani Rent Transparency Portal, wanda zai bai wa jama’a damar tantance gidaje, masu gidaje da dillalan da aka ba lasisi, da kuma sanin farashin hayar da aka amince da shi.
Ya ce za a rika bitar farashin haya lokaci zuwa lokaci bisa la’akari da hauhawar farashi, kuɗin gini, darajar gidaje da yanayin kasuwar haya.
“Manufar ba ita ce azabtar da masu gidaje ba, sai dai samar da kasuwar haya mai adalci, inda ’yan haya za su biya kuɗi na gari, yayin da masu gidaje su samu riba mai kyau,” in ji shi.
