Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi watsi da abin da ya kira “naɗin sarauta” da ake yi wa wasu yan takara a matsayin maslaha a dukkan kujerun zaɓe a jihar Gombe.

A wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed ya sanya wa hannu a madadin mambobi da magoya bayan ƙungiyar Pantamiyya Movement, ya ce babu ingantacciyyar maslaha a doka matuƙar ba a haɗa dukkan yan takarar da suka sayi fom ɗin tsayawa takara ba.

HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim

Sanarwar ta ce dokar zaɓe ta ƙasa ta 2026 ta tanadi hanyoyi biyu kacal da jam’iyyun siyasa za su bi wajen zaɓen yan takara, waɗanda suka haɗa da maslaha da kuma zaɓen kai tsaye.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version