Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta duba yiwuwar dakatar da yaƙin neman zaɓen 2027 a wasu jihohin arewa guda takwas da ke fama da matsalar tsaro.

Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi ne ya gabatar da ƙudurin a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda ya ce akwai buƙatar a duba yanayin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a ƙasar.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ningi ya ce bai kamata ƴan majalisar su kauda kai daga matsalar tsaron da ke damun wasu sassan ƙasar saboda su suna zaune a Abuja.

“Mataki ne da ya zama wajibi mu ɗauka. Ko dai a dakatar da duk wasu tarukan siyasa a faɗin ƙasar ko kuma a dakatar a jihohin da ke da matsala,” in ji Sanata Ningi.

Sanatan ya lissafo johohin Borno, Plateau, Bauchi, Benue, Niger, Sokoto, Kebbi da wasu sassan Kano.

“Ya kamata mu dakatar da duk wasu abubuwan siyasa a waɗannan jihohin har sai lamuran tsaro sun daidaita,” in ji shi.

Gargaɗin na Sanata Ningi na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, ciki har da hare-hare kan sansanonin soji a ƙasar da kuma garkuwa da mutane.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version