Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa akwai wani sabon shiri na haɗa shi da aikata laifuka domin sake tsare shi.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar, ya bayyana cewa wannan yunkuri na daga cikin wani tsari na ɓata masa suna da kuma hana shi samun ‘yanci.

Sanarwar ta kuma ce El-Rufai na duba yiwuwar ɗaukar matakin shari’a kan jaridar The Nation, bisa wani rahoto da ta wallafa da ke danganta shi da wani hari da aka kai gidan wani shaida a Kaduna.

Rahoton jaridar ya ambato wani shaida mai suna Mohammed Umar Karage, wanda ya ce wasu ‘yan bindiga sun kai masa hari, tare da hasashen cewa hakan na da alaƙa da shari’ar da yake bayar da shaida a cikinta.

Sai dai ɓangaren El-Rufai ya ƙaryata wannan zargi, yana mai cewa an tsara rahoton ne domin ɓata masa suna da kuma shafar buƙatarsa ta neman beli a kotu.

Sanarwar ta tuno cewa a watan fabrairu, an yi yunkurin kama shi a filin jirgin saman Abuja bayan dawowarsa daga birnin Alkahira, kafin daga bisani ya amsa gayyatar hukumar EFCC, wadda ta tsare shi, sannan aka miƙa shi ga ICPC.

Tsohon gwamnan ya ce shi ɗan ƙasa ne mai bin doka, kuma ba shi da wata alaƙa da harin da ake zargi, yana mai jaddada cewa za su ɗauki matakin shari’a kan duk wani abin da ya shafi ɓata masa suna.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version