Gwamnatin Jihar Kano ta musanta zargin cewa tana da hannu a wata yarjejeniyar musayar fili da ake dangantawa da Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kano (FGC Kano).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na Gwamnan jihar, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Litinin.

A cikin sanarwar, gwamnatin ta bayyana karara cewa ba ta da hannu a kowace irin yarjejeniya, tattaunawa ko wata alaka da aka yi dangane da wannan fili.

Ta kuma jaddada cewa Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Kano tana karkashin ikon Gwamnatin Tarayya ne ta hannun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, wadda ita kadai ke da alhakin yanke duk wani hukunci da ya shafi makarantar.

Gwamnatin jihar ta kara da cewa duk wani yunkuri na alakanta gwamnatin ko mukarraban gwamna Abba Kabir Yusuf da wannan zargin ba shi da tushe, kuma y yaudarar jama’a ne.

Duk da amincewa da damuwar da wasu ‘yan kasa suka nuna, gwamnatin ta bukaci kafafen yada labarai da su rika bin ka’idojin gaskiya, adalci da aikin jarida nagari, tare da kaucewa wallafa rahotannin da ba a tabbatar da su ba.

A karshe, gwamnatin ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da gaskiya, bin doka da kuma kare muradun jama’a.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version