Dubban al’ummar jihar Kano sun fito kan tituna a ranar Asabar domin tarbar Gwamna Abba Yusuf bayan dawowarsa daga Abuja, inda ya gana da shugabannin jam’iyyar APC.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya kuma kasance cikin tawagar APC da ta je jihar Bauchi domin jawo Gwamna Bala Mohammed ya koma jam’iyyar daga PDP, duk da cewa har yanzu bai bayyana matsayinsa ba.

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

Tarbar ta biyo bayan sauye-sauyen siyasa a Kano, ciki har da ficewar Rabiu Musa Kwankwaso daga NNPP zuwa ADC tare da hadewa da Peter Obi da sauran ‘yan adawa.

Magoya bayan Yusuf sun cika tituna daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano zuwa gidan gwamnati, suna daga tutoci tare da rera wakokin goyon baya, lamarin da ya haifar da yanayi irin na shagali.

Wasu mazauna Kano sun bayyana tarbar a matsayin daya daga cikin mafi girma a baya-bayan nan, suna mai cewa hakan na nuna karfin goyon bayan da gwamnan ke da shi a kasa.

Masu sharhi kan siyasa sun ce sauye-sauyen da ke gudana, musamman sauyin da Kwankwaso ya yi, sun kara tsananta adawar siyasa a Kano, wadda ke da muhimmanci wajen zaben shugaban kasa a Najeriya.

Wasu mazauna Kano sun kuma nuna cewa wannan goyon baya zai bayyana a zaben 2027, inda suka yi alkawarin mara wa Yusuf baya domin ci gaba da ayyukansa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version