Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya fuskanci suka daga jama’a bayan ya ce da zai samu dama da ya “harbi” mai gabatar da shirin talabijin, Seun Okinbaloye na Channels TV.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Wike ya yi furucin ne yayin da ya ke mayar da martani kan wani wani tsokaci da ɗan jaridar ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin din dangane da siyasar Najeriya yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Dandazon jama’a sun tarbi Gwamna Yusuf a Kano
Jaridar ta rawaito cewa ko da ya.ke daga bisani Wike ya ce ba wai har zuci ya faɗi maganar ba, kalaman nasa sun jawo alla-wadai daga kungiyoyin kare ‘yancin ƴan jarida da farar hula, waɗanda suka bukaci ya ba da hakuri.
Kungiyoyin sun ce irin wannan furuci na iya tsoratar da ‘yan jarida tare da kawo cikas ga dimokuradiyya.
Lamarin ya kuma jawo muhawara a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka soki kalaman a matsayin marasa dacewa da mukamin gwamnati.
