Mataimakin gwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar NNPP Aminu Abdussalam Gwarzo yayi murabus.

A cewar kafar yada labaran Arewa Updates wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiya Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar.

Hisbah ta kama wasu matasa a otel a Kano

Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma bai wa ofishin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.

Sanarwar ta ce murabus ɗin ba yana nufin amincewa da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi ba, inda Mataimakin Gwamnan ya jaddada cewa yana da tsabtataccen tarihi a aikin gwamnati.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa zai mai da hankali wajen ƙarfafa ƙungiyar Kwankwasiyya da tsara dabarun siyasa gabanin zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta buƙaci magoya bayanta da al’ummar jihar da su kasance masu bin doka tare da ci gaba da goyon bayan shugabanci nagari..

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version