Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da sa ido kan kashe kuɗaɗen gwamnati, a Najeriya, SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya NBET, bisa zargin karkatar da Naira biliyan 128.

‎SERAP ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan zarge-zargen da ke cikin rahoton Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya da aka wallafa a watan Satumba na bara.

‎“Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai ‎ ‎ ‎—Comrade Abbas Ibrahim

‎Ƙungiyar na neman kotu ta tilasta wa waɗanda ake ƙara su yi cikakken bayani kan kuɗin, tare da bayyana sunayen jami’ai ko kamfanonin da suka amfana da su.

‎A cewar SERAP, cin hanci da rashawa a ɓangaren wutar lantarki na ƙara jefa ’yan Nijeriya cikin duhu, inda ake fama da rushewar layin wuta da kuma biyan kuɗaɗen wuta masu tsada.

‎Sai dai har yanzu ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version