Ƙungiyar Dispute Resolution and Development Initiative (DRDI) ta Kaddamar da horon Kwana daya don wayar da kan al’umma da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gabatar da kasafin kuɗi, a kananan hukumomi.
Babban Daraktan Ƙungiyar Tabbatar da Dimokuraɗiyya da Zaman Lafiya ta DRDI, Dr. Muhammad Mustapha Yahaya, ya ce ƙungiyar ta kaddamar da shirin wayar da kan al’umma kan yadda ake gabatar da kasafin kuɗi da kuma yancin da aka ba su a harkokin ƙananan hukumomi da siyasa gaba ɗaya.
Gwamnonin Arewa sun bukaci a dakatar da ayyukan hako ma’adanai domin shawo kan matsalar tsaro
A cewarsa, aikin nasu a yanzu ya fara ne a jihohin Kano da Jigawa, inda suka zaɓi kananan hukumomi uku-uku domin gudanar da bincike da tattaunawa da jama’a kan bukatun su, da yadda za a haɗa su cikin kasafin kuɗin shekara.
Dr. Mustapha ya bayyana cewa babban manufar shirin shine bada dama ga al’umma su bayyana bukatunsu tun kafin a kammala kasafin kuɗi, domin a tabbatar da cewa kuɗin da ake kashewa ya amfanar da jama’a.
Ya ce“Gaba dayan shirin an tsara shi ne domin wayar da kan al’umma su san yadda ake gabatar da kasafin kuɗi da kuma yancin da aka basu wajen tsoma baki a harkokin ƙananan hukumomi da siyasa gaba ɗaya. Wannan yana taimakawa wajen ganin gwamnati ta saurari bukatun jama’a kafin kasafi ya fita.”
Babban Daraktan ya nuna damuwa kan ƙarancin kuɗin da ake warewa bangaren kiwon lafiya da ilimi, wanda zai iya kawo koma-baya a zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Ya kara da cewa Rashin bibiyar kasafin kuɗi daga al’umma na daga cikin matsalolin da ke kawo gibin fahimta tsakanin gwamnati da jama’a.
Rashin shigar da bayanan jama’a cikin kasafin kuɗi na kara matsalar rashin dacewa tsakanin abin da al’umma ke bukata da abin da gwamnati ke aiwatarwa.
Jinkirin majalisu wajen sahale kasafin kuɗi na haifar da shiga sabuwar shekara ba tare da kasafi ba, lamarin da ke ƙara yawan cin hanci da tabarbarewar tattalin arziki.
Dr. Mustapha ya shawarci gwamnati da majalisun dokoki su ɗauki matakan gaggawa wajen tabbatar da sahale kasafin kuɗi a kan lokaci da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata, tare da sauraron ra’ayoyin al’umma .
Ya ce hakan ne kawai zai taimaka wajen tabbatar da dimokuraɗiyya mai inganci, ci gaban ƙananan hukumomi, da zaman lafiya a Najeriya.

